Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (IEA) ta ce, kasashen Yamma su daura damarar tunkarar abin da ka iya biyo baya, saboda akwai yiwuwar kasar Rasha ta yanke tura musu iskar gas.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ruwaito Babban Daraktan IEA, Fatih Birol na cewa, “Ba na ganin Rasha za ta daina neman dalilai nan da can da kuma uzurorin da za su sanya ta ci gaba da rage iskar gas din da take tura wa yankin Turai, mai yiwuwa kuma ta yanke tura gas din baki daya.”
- ‘Yan sanda a Katsina sun ceto budurwa daga hannun ‘yan bindiga
- INEC ta amince da kara wa’adin sabunta rajistar zabe
Birol ya kara da cewa, “Wannan ne dalilin da ya sa Turai na da bukatar samar da wani tsari mai karko” wanda zai taimaka masa wajen ci gaba da samun iskar gas din.
Ya ce, rage hannu da Rashar ta yi wajen tura iskar gas zuwa Turai, watakila ta yi hakan ne saboda cim ma wata manufa ta siyasa.
Da ma dai Kungiyar Tarayyar Turai ta kakaba wa Rasha takunkumi kan batun man fetur da ma’adinin kwal, amma ta daga mata kafa a bangaren iskar gas saboda yawan dogaron da takan yi da ita wajen samun gas din.