Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Stephen Keshi ya ce ya gwammace a yi wasan neman gurbin zuwa cin kofin Afirka da zai gudana a ranar Laraba 15 ga wannan wata a tsakanin Najeriya Super Eagles da kuma Sudan a Kaduna maimakon a filin wasa na kasa da ke Abuja.
Kocin ya ce saboda irin halin da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles ta shiga a wannan lokaci akwai bukatar ta buga wasanta na biyu da Sudan a Kaduna maimakon Abuja saboda samun magoya baya masu yawa da za su fito kwansu da kwarkwatarsu don marawa kungiyar baya.
Ya ce duk da yake filin wasa na kasa da ke Abuja ya fi na Kaduna kyau fa dadi, amma da wuya magoya bayan da za su kalli wasan a Abuja su kai na Kaduna yawa saboda mafi yawan ’yan Abuja sun gwammace su kalli wasan a akwatunan talbijin ne maimakon halartar filin wasa.
“Da wuya a cika filin wasa na kasa idan aka yi wasan a Abuja saboda mafi yawan magoya bayan kungiyar Super Eagles da ke Abuja ba su cika halartar filin wasa don ganin yadda za ta kaya ba, sun gwammace su zauna a gidajensu don kallon yadda wasan zai kaya a akwatunan talbijin dinsu”, inji Keshi.
Kocin ya kara da cewa, a halin yanzu babu abin da kungiyar take bukata da ya wuce addu’a da kuma samun magoya bayan da za su karfafa wa ’yan kwallon gwiwa a ranar wasannin.
Idan aka buga wasan gobe, a ranar Laraba mai zuwa ne kuma ake sa ran za a yi wasa na biyu a tsakanin kasashen biyu. Sai dai ya zuwa wannan lokaci Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa NFF ba ta tantance ko ta amince a yi wasa na biyu a tsakanin Najeriya da Sudan a Kaduna ko a’a ba.
…Mai yiwuwa a yi wasan Najeriya da Sudan karo na biyu a Kaduna
Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Stephen Keshi ya ce ya gwammace a yi wasan neman gurbin zuwa cin kofin Afirka da zai…