Wani matashi mai suna Hamza Musa Muhammed da ake zargi da yaudarar mutane yana yi musu fashi ya gurfana a gaban Babbar Kotun Majistare ta Biyu da ke Gombe fadar Jihar Gombe.
A ranar Alhamis din makon jiya ne ’yan sanda suka gurfanar da Hamza Musa Muhammed, mai
shekaru 37 da a gaban kotun da ke Unguwar Tumfure, bisa zargin fashi da makami da jawo rauni
da yunkurin kisan kai.
dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Habibu danjuma Juwara, ya shaida wa kotun cewa a ranar 4 ga Oktoban shekara ta 2013, Hamza wanda ke zaune a Unguwar Arawa ya tona rami a falon gidansa sannan ya gayyaci wani mai sayar da motoci mai suna Yusuf Muhammed Madugu na kamfanin sayar da motoci na Aji Motors da sunan zai sayi mota a wurinsa, inda ya buga wa Yusuf Madugu karfe a kai ya fadi sumamme sai ya dauka ya mutu ne, ya dauke masa wayar salula kirar Android Samsung da kudinta ya kai Naira dubu 45 da kuma Nokia ta Naira dubu 15 ya kwashe masa Naira dubu 12 a aljihunsa.
Ya kuma ce a wannan rana ya sake kiran wani mai suna Mohammed Shu’aibu, zuwa gidansa shi ma ya buga masa wannan karfe a kai, dukansu ba su mutu ba, amma sun samu munanan raunuka a kai, kuma ganin asirinsa zai tonu ne ya gudu daga Gombe a ranar ya bar wata motarsa kirar Honda Prelude Ja marar lamba da ake zargin ita ma ta sata ce kafin a gano shi a wata maboyarsa a Kaduna ranar 2 ga Agustan bana.
A cewar dan sandan, aikata hakan laifi ne da ya saba wa sassa na 298 da 246 da 95 da 319 (A) na kundin laifuffuka da hukuncinsu na Penal Kod.
Da kotu ta waiwayi wanda ake zargin, ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, inda Alkalin Kotun Mai shari’a Japheth Maida, ya tura shi gidan kurkuku zuwa 31 ga Agusta don ci gaba da sauraron shari’ar.