Rikicin ya faro ne saboda rasit din N50 na haraji da mai tura baron ya ki yanka daga jami’in karbar harajin.
Shaidu sun ce a kan haka ne mai karbar harajin ya ture baron kayan ciki suka zube a kan hanya.
- Rabin mutanen Arewa maso Gabas na da matsalar kwakwalwa —Masana
- Jerin hatsarin jiragen sojin Najeriya a 2023
Mutane sun nemi su kwaci mai karbar harajin, amma mai tura baron bai bari ba sai da ya tabbatar ya daina motsi.
Daga bisani kuma ya soka wa kansa wukar a wuya, shi ma ya ce ga garinku nan.
Lamarin ya jefa yankin Mission Road da ke Karamar Hukumar Oredo cikin zullumi, inda masu aikin karbar haraji suka janye suna neman sai gwamnati ta tabbatar da tsaron lafiyarsu.
Wani ganau dai ya koka kan yadda masu karbar harajin ke cin mutuncin jama’a a garin na Benin.
Ya ce “Babu dalilin kisan amma shi ma mai karbar harajin bai kyauta ba, mutane na cikin matsin rayuwa.
“Ba a san da harbebeyar wuka a jikin mai tura baron, kawai ga aka yi ya ciro ta ya soka masa.
“An so a kama shi amma ya ce duk wanda ya matso shi zai kashe shi, kafin ya soka wa kansa wukar.”