✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai tabin hankali ya kashe mutum 8 a Adamawa

Sai dai daga bisani shi ma wasu mutane sun kashe shi

Wani mutu mai fama da larurar tabin hankali ya kashe mutum 8 sannan ya jikkata wasu da dama a gundumar Kate-Gamji da ke Karamar Hukumar Shelleng a Jihar Adamawa.

Mutumin, wanda aka ce sunansa Ali Denham dai ya yi amfani da diga ne wajen saran mutanen da daren Laraba, inda ya kashe takwas daga cikinsu, ya jikkata wasu uku, kafin shi ma daga bisani wasu su kashe shi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Sulaiman Nguroje, ya gargadi jama’a da su guji ajiye masu tabin hankali a gidajensu, musamman wadanda ya kamata a ce suna asibitin kwakwalwa.

Ya ce mutumin ya kashe mutu takwas sannan ya ji wa wasu da dama rauni, kafin daga bisani shi ma wasu da ba san ko su wane ne ba su kashe shi.

Sai dai Kakakin ya ce tuni jami’ansu suka fara bincike a kan lamarin.

A wani labarin kuma, Shugaban Karamar Hukumar da abin ya faru ta Shelleng, Abubakar Musa Abba, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan da kisan ya shafa, inda ya bukace su da su dauki lamarin a matsayin kaddara daga Allah.