✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai shekara 25 da siffar tsoho

Matashin ya yi kama da mai shekara 40, duk da cewa yana da shekara 25 ne kacal.

Wani matashi mai shekara 25 da ke birnin Zhengzhou a kasar China ya samu shahara a wajen mabiya shafuffukan sada zumunta na Intanet ta minti biyar, bayan da hotunansa sun ta zagawa da siffar da ba a saba gani ba.

Matashin mai suna Zhu, wanda kamanninsa ya sauya zuwa siffar tsoho da ba a saba gani ba, duba da shekarunsa.

Bayanai sun ce, matashin ya yi kama da mai shekara 40, duk da cewa yana da shekara 25 ne kacal.

Hotunansa sanye da tufafin da ba na zamani ba da tabarau da kuma askin tsofaffi sun ja hankalin jama’a sosai a shafin Twitter na Weibo na kasar China, lamarin da ya jawo kalaman ban-dariya.

Matashin wanda ma’aikaci ne a Zhengzhou ya ce, yana wasannin motsa jiki tare da yin barkwanci da kamanninsa, inda ya ce a duk lokacin da ya nemi wani ya zama abokinsa kafar sadawar zamani, yakan samu martanin da ke nuna shakku a kan shekarunsa, inda mutane da dama suke ganin karya yake yi.

Ya ce, tufafin da yake sanye da su ba su da kyau, na aiki ne, duk da haka da yawa sun musanta tare da kin yarda.

Yayin da akasarin masu amfani da Intanet suke yin tsokaci cikin raha game da kamanninsa, da yawa sun shawarce shi ya rage kiba domin ya yi kusa da ainihin shekarunsa.

“Yana da kiba ne. Lokacin da ka rage nauyi, za ka zama karami,” in ji wani da ya yi tsokaci a kan kamannin nasa.