Wani mai maganin gargajiya, Ismail Usman, ya ɗirka wa kansa harsashi a lokacin da yake gwajin maganin bindiga.
Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin Kuchibiyi da ke Karamar Hukumar Bwari a Abuja.
- Babu ja da baya kan sake fasalin tattalin arzikin Najeriya — Tinubu
- Isra’ila ta soma saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon
Wani mazauni a yankin, Samson Ayuba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da mutumin ya ɗirka wa kansa harsashi a cikin a ƙoƙarin gwada ingancin maganin bindigar da ya haɗa.
Samson ya ce sai makwabta ne suka yi gaggawar mutumin asibiti bayan ya faɗi ƙasa wanwar yana shure-shure.
Rundunar ’yan sandan Abuja ta bakin mai magana da yawunta, Joesephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin.
Josephine ta ce sun samu kira kan cewa wani mai maganin gargajiya ya harbi kansa a daidai lokacin da yake gwajin ƙarfin maganin bindigar da ya haɗa.
Ta bayyana cewa a yayin da yake gwajin sai maganin ya gaza ba shi kariya inda ya ɗirka wa kansa harsashi.
Josephine ta ƙara da cewa tuni aka garzaya da mai maganin gargajiyar asibitin Kubwa domin duba lafiyarsa kafin daga bisani aka aika shi asibitin ƙwararru da ke Gwagwalada domin samun ƙarin kulawa.
Jami’an tsaron sun bayyana cewa bayan sun gudanar da bincike a gidansa, sun gano wata bindigar gargajiya da layu a gidansu waɗanda ya yi amfani da su wurin gwajin maganin bindigar.
‘Yan sandan sun kuma ce a halin yanzu suna ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba da kuma yunƙurin kashe kansa.