✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai labari

Wani Bakano ne ma’abocin sauraron rediyo, a kowane lokaci za ka same shi ya kasa kunne yana sauraron labarai gami da kade-kade. Ana cikin wannan…

Wani Bakano ne ma’abocin sauraron rediyo, a kowane lokaci za ka same shi ya kasa kunne yana sauraron labarai gami da kade-kade. Ana cikin wannan hali sai wannan katuwar rediyo ta samu matsala ta lalace, ya yi tunanin ko batirin rediyon ne ya cinye. Ya sayo sababbi ya sanya amma shiru ba wani motsi. A haka ya hakura, ya je ya samu wani wuri cikin dakinsa ya rataye radiyon nan, kafin ranar kasuwa ta zagayo ya kai ta a gyara masa. Ashe hanyar wadansu manyan beraye ce ya rataye wannan katuwar rediyon tasa. Koda ganin haka sai berayen nan suka rika shiga ciki suna yin sheka. Wata daga cikinsu za ta haihu, duk abin da da ke faruwa shi dan Kano bai sani ba. Ranar kasuwa na zagayowa,dan fillo ya sungumi rediyo sai wurin mai gyara. Yana zuwa kuwa ya ci  sa’a ba layi a wurin mai gyaran. Mai gyara ya kama rediyo ya kwance. Yana budewa sai kuwa wani katon bera ya fito a guje. Ganin haka Bafulatani ya sabi sanda ya bi katon beran nan a guje, yana fadin cewa: “Jama’a ku tare mini, ga mai ba da labarai zai gudu.”
Daga Nura Suleja Neja, 08078983237