Wani rahoto da shafin da ke bin diddigin farashin fetur a duniya ya fitar na nuna cewa Libya ce ƙasar da tafi kowacce arhar man a Nahiyar Afirka.
Rahoton ya nuna cewa zuwa ranar 16 ga watan nan na Satumba, 2024, a kan Dala 0.032, kwatankwacin N52 na kuɗin Najeriya ake sayar da litar fetur a Libya, ƙasar da ta shekara 13 cikin yaƙin basasa.
Tun bayan hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar Libya na mulkin soji, Mu’ammar Gaddhafi, a watan Oktoban shekarar 2011 ta ƙasar ke fama da yaƙe-yaken cikin gida.
Rahoton ya nuna farashin litar fetur a Najeriya, ƙasar da ta fi arzikin mai a Afirka, ya ninka na Libya sau aƙalla 16.
Ƙasashen da ke biye da Libya a arhar fetur a Afirka su ne: Masar (Dala 0.279) sai Algeria (Dala 0.342) Sannan Angola (Dala 0.351).
Rahoton ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar wajen arhar fetur a Afirka.
A halin da ake ciki, mafi ƙarancin farahsin litar fetur a Najeriya shi ke Naira 879 a farahsin gwamnati.
’yan kasuwa na sayar da shi a kan kimanin N1,000 a yayin da masu bumburutu ke sayarwa kimanin N1,600.
Rahoton ya nuna cewa ƙasar mafi tsadar man fetur a Afirka ita ce Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a kan Dala 1.83.
Sauran su ne:
- Senegal – $1.646
- Seychelles – $1.595.
- Zimbabwe – $1.590.
- Morocco – $1.527.
- Uganda – $1.475.
- Malawi – $1.458
- Côte d’Ivoire – $1.455
- Kenya – $1.453.
- Saliyo – $1.448.
Tsadar mai a Najeriya duk da kasancewarta kasa mafi arzikin mai a Afirka ta sa al’ummar ƙasar sukan gwamnati, inda suke ganin ba haka ya kamata ba.