Wata mai koyon sana’ar kitso da gyaran gashi ta sace jariri dan wata shida a shagon mahaifiyarsa da ke Kasuwar Kure Ultra-Modern a Minna, Jihar Neja.
Mahaifin jaririn, Mista Chikezie Stanley Chuks, ya bayyana cewa mai koyon sana’ar gyaran gashi a wurin matar tasa ce ta sace jaririn nasu a shagon.
- An kafa tarihin sanya hijabi karon farko a Gasar Kofin Duniya ta Mata
- NAJERIYA A YAU: IPOB Na Kassara Tattalin Arzikin Kasuwanci A Dalilin Dokar Zaman Gida
Ya ce “An sace jaririnmu mai wata shida a duniya, mai suna Chinedu a shagon matata na gyaran gashi da ke Kasuwar Kure Ultra-Modern da ke Minna,” in ji shi a shafinsa na Facebook.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, wadda ta sace jaririn “ta je shagon matata ne a matsayin mai koyan sana’ar gyaran gashi, amma sai ta buge da dauke jaririn ta tsere da shi a ranar Asarar 23 ga watan nan na Yuli.
“Duk wanda ke da wani bayani da zai taimaka, ya sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa da shi, ko kuma ya tuntubi wannan lambar wayar: 07033186837.”
Wakilinmu ya yi kokarin tuntubar mahaifin jaririn da aka sace domin samun karin bayani, amma sai dai ba a amsa wayar ba, har zuwa lokacin kammala wannan rahoton.
Mun tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, kan batun, amma ya ce ba a sanar da rundunarsu game da lamarin ba a hukumance.
DSP Abiodun ya kara da cewa “Ina shawartar iyayen da su kai rahoto zuwa Babban Caji Ofis da ke unguwar GRA, wanda ke kuka da Kasuwar Kure, domin su dauki bayanai da zurfafa bincike domin ceto jaririn da kuma cafke wadda ake zargi.”