Mai kamfanin sada zumunta na Facebook, WhatsApp da Instagram, Mark Zuckerberg, ya tafka asarar sama da Dala biliyan bakwai a cikin awa shida da kafofin suka daina aiki.
Zuckerberg, wanda ke cikin shahararrun attajiran duniya, ya tafka wannan asarar ce zuwa ranar Talata bayan daukewar kafofin sada zumuntar — asarar da ta haura Naira tiriliyan uku.
- Dangote ne kadai ya shiga jerin attajiran duniya na Bloomberg daga Najeriya
- Dambatta, NCC da kokarin zakulo Zuckerbergs din Najeriya
Ana hasashen daukewar kafofin sada zumuntar a ranar Litinin ta hana mutane biliyan uku da rabi da ke amfani da shafukan damar shiga a cikin ’yan awanni.
Hakan ya sa shugaban kamfaninin kuma wanda ya kirkiro Facebook, Zuckerberg, ya ba wa al’ummar duniya hakuri game da abin da ya faru.
A yanzu dai kafofin sun dawo, amma daukewarsu a ranar Litinin ta ja wa mai kamfanin sauka zuwa mataki na biyar a cikin masu kudin duniyar kamar yadda kafar watsa labarai ta Bloomberg ta wallafa.
Wannan shi ne karo na biyu da kamfanin ya samu tangarda a shekarar 2021.
Daga watan Satumba zuwa yanzu, Zuckerberg, wanda yawan dukiyarsa ta kai Dala biliyan 140, ya takfa asarar da ta hausa Dala biliyan 19.
Bloomberg ta ruwaito cewa daukewar kafofin sada zumutanar ta sa hannun jarin kamfanonin uku da Facebook ke mallaka karyewa da kashi 5 cikin 100 a ranar Litinin bayan karyewar kashi 15 cikin 100 da aka samu a tsakiyar watan Satumba.