An gurfanar da matar nan da ake zargi da kai ’ya’yanta mata wurin masu garkuwa da mutane suna lalata da su a gaban Kotun Majistare da ke Fada a birnin Zariya.
Matar mai suna Maryam Abubakar, ana tuhumarta ce da kitsawa da tsara yin garkuwa da mutane da safarar ’ya’yanta zuwa dajin Galadimawa, inda take kai wa Isa Dan Wasa don yin lalata da su, wanda hakan ya saba wa Sashi na 248 na kundin Manyan Laifuffuka na 2007. An gurfanar da ita ce tare da Hajara Abubakar.
- Yadda barawon kananan yara ya fada komar ’yan sanda
- Kotu ta ci ’yan tumatir a kasuwar Sabon Gari tarar N50,000
Haka an gabatar da Fatima Jibrin (Ummi) wadda ke zaune a Tohu a Karamar Hukumar Sabon Gari tare da Lawisa Hassan da wani mai suna Muslim Abunakar bisa hada baki da masu garkuwa da mutanen wadanda suke zaune a dajin Galadimawa a Karamar Hukumar Giwa da kuma yunkurin satar mutane wadanda suka saba wa Sashi na 247 kashi na 2 da Kundin Final Kod na shekarar 2007 da aka gyara.
Sai kuma Jummai Ibrahim Nuhu wadda ke zaune a Tankarau da ake zargi da bayar da bayanai ga saurayinta mai suna Idris Ibrahim, inda ta ba shi bayani kan Alhaji Kadade kuma laifin ya saba wa sashi na 248 kashi na 1 na kundin Final Kod.
Lawisa Hassan da Muslim Abubakar, mazaunin Sakadadi ana tuhumar su ne da laifin hada baki da yin garkuwa tare da yin fyade.
Wadanda ake tuhumar an ce sun hada baki ne suka yaudari wata Hadiza Musa suka kai ta wajen wani Rashidu Danfari shugaban dabar masu garkuwa da mutane ya yi lalata da ita wanda hakan ya saba wa sashe na 59 da 241 da 269 na dokokin Final Kod na Jihar Kaduna.
Sagir Yusuf wanda ake wa lakabi da Mai-Zuma, ana tuhumarsa ce da yin garkuwa da mutane, inda wani mai suna Hamza Abdulhamid da ke Igabi ya ce kimanin wata uku da suka gabata masu garkuwa da mutane sun je gidansa suka tafi da shi cikin dajin kuma suka bukaci a ba su Naira miliyan 30, amma aka daidaita a kan Naira miliyan biyu kuma ya gane Sagir Yusuf yana daya daga cikinsu.
Sai Muslim Abubakar wanda aka gurfanar bisa laifin bayar da bayanan karya don yaudarar mutane.
Dukkansu Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna ne yake karar su kuma kotun a karkashin Mai shari’a Zainab Garba Ahmad ta dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga Maris, 2022.
A ranar 21 ga Disamban bara ce ’yan sanda na musamman masu yaki da ’yan fashin daji da ’yan ta’adda (IRT), suka samu nasarar kama wadanda ake zargin su da safarar ’yan mata suna kai su wajen ’yan bindiga da ke dajin Galadimawa suna lalata da su.