Wata mata mai suna Shema’u Labaran, ta rasu a Asibitin Abdullahi Wase da aka fi sani da Asibitin Nassarawa a Jihar Kano, saboda kudin da mijinta ya tura ta intanet bai shiga asusun asibitin da wuri ba.
Maigidan margayiyar, Malam Bello Fancy, ya ce sabuwar dokar sauyin kudi ce ta kai ga rasa matarsa, domin da tsoffin kudinsa ya je a hannu amma aka ki karba a asibiti, kudin da ya tura ta intanet kuma ya ki sauka asusun asibitin a kan lokaci.
- Boko Haram na shirin kai wa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari —DSS
- Yadda kogin Jami’ar ABU ya ci dalibai ’yan gida daya
Ya ce bayan ya tura kudin farko, likitocin suka ce ba za su duba matar ta sa ba har sai sun shigo asusun asibitin, lamarin da ya sa suka shafe sa’o’i uku suna jiran tsammani.
Ya shaida wa Gidan Rediyan Freedom da ke Kano, cewa nakuda matar tasa take yi aka kai ta asibitin kuma da kafarta ta tako, amma sai da ta fita hayyacinta kafin a duba ta.
“Da kafafunta ta shiga asibitin, amma kan su ga taransafar ciwo ya karu har ta fara zubar da jini, amma duk da haka ba su duba ta ba sai bayan kusan sa’oi uku da suka ga shigar kudin asusunsu.
“Daga nan ne suka ga ba za ta iya haihuwa da kanta ba sai an yi mata aiki.
“Suka ce sai na sake biyan wani kudin, na amince da sake biya ta taransfar saboda sun ce ba su da POS, shi ma dai haka ya shafe sa’o’i ukun kafin su gani su yi mata aikin.
“Kafin a yi mata aikin ta gama galabaita sosai, ana gamawa aka ciro dan ya rasu, ita ma matar tawa ta rasu”, in ji Fancy.
To sai dai Shugabar Asibitin, Dokta Rahila Garba ta musanta zargin, inda ta ce ba gaskiyar abin da ya faru magidancin ya fada ba.
To sai dai sauran marasa lafiya da suka je asibitin neman magani sun tabbatar wa Aminiya cewa lamarin fa da gaske ya faru, domin ko su ma da taransfar suka biya, kuma sai an ga kudin sun shiga ake ba su kulawa.
A nasa banagren Kakakin Hukumar Kula da Asibitocin Kano Malam Ibrahim Abdullahi ya ce sun samu labarin aukuwar lamarin, kuma sun fara bincike.