Duk Duniya an yi amannar cewa arzikin da Najeriya take da shi a halin yanzu bai kamata a ce ana fama da tsadar rayuwa a sassan kasar ba. Domin kuwa masana tattalin arziki sun yi sharhi da bayar da shawarrarin kan yadda za a inganta rayuwar al’ummar kasar nan.
An kwace miliyoyin Naira daga hannun barayin gwamnati an jibge a asusun gwamnati, amma har yanzun babu wani sauyin da talaka zai bugi kirji ya ce ya gani a zahirance. Domin kuwa wallahi abin da ake yi a waccan gwamnatin har yanzu bai sauya ba ana yi, alal misali: Duk karshen wata akwai alawus-alawus da Sanatoci ke karba domin su yi aiki a mazabunsu, amma ba sa yi, ko akwai wanda zai fada mana cewa ga ayyukan da Sanatan su yake yi duk karshen wata?
Idan ka ji Sanata ya yi abin a zo a gani to wani ne aka yi hanya ya samu aikin gwamnati ko ya yi rabon kuddi ga wasu kebabbu cikin jama’arsa. Zan iya cewa tun bayan darewar gwamnatin APC babu wani abin da suke yi illa rabon katin ‘D E’ ga masu niyyar zuwa jami’a ko kuwa biyan kudin tallafin karatu “Sholarship.”
Don haka duk wani yunkurin da Shugaba Buhari yake yi da nufin ceto Najeriya daga halin da gwamnatin baya ta tsunduma kasar ciki, ba tare da an yi garambawul a ma’aikatun gwamnati ba, wallahi shirme ne, kuma a hakan za a cigaba da zama tare da wadannan kusoshin a birnin Abuja, sa’annan ana damawa da su a al’amuran gwamnatin duk da cewa an san su ne gurbatattun.
Domin kuwa a yanzu haka galibin al’ummar Najeriya ba su san me ake nufi da shugabanci ba. Da sun sani na yi imanin cewa da tuni an yunkura wajen ganin an sauke wadannan masu hana ruwa gudun. Kana bugu da kari ’yan kasar ba sa amfani da iliminsu wajen iya tantance kamshi da karni, misali: mutum ya yi karatu ya iya rubutu sa’annan kusan kullum iya bibiyar kafafen yada labarai domin sanin halin da duniya take ciki, amma da zarar wani mai sauraren rediyo ya riske shi ya ce: ‘’Ai dazu da sassafe na saurari gidan Rediyon Faransa na ji Sanata wane ko Dokta Wane ya soki Gwamnatin Buhari, inda ya ce har yanzu ba a ida kwato kudin da barayi suka yi sama da fadi da su ba.’’ Shi ke nan daga nan za a ci gaba da yada zancen tsinuwa ga wannan mutumin.
Don haka jama’a ya kamata mu yi amfani da tunaninmu da kuma iliminmu domin iya tantance jita-jita da kuma zancen kanzon kurege.
Sauyin gwamnati: Idan aka yi maganar gudummuwar matasa a Gwamnatin Buhari sanin kowane masu hulda da kafafen yada labarai na kasashen ketare matasa ne, kuma sun taka rawar gani tun daga shekarar 2010 har zuwa 2015 suna suka, tare da caccakar Gwamnatin PDP karkashin Shugaban Jonathan, har aka kai ga ganin karshen wannan kuncin rayuwa da talakawan kasa ke ciki, cikin ikon Ubangiji a ka yi sa a a zaben 2015 Gwamnatin PDP ta zama tarihi.
To, don a yanzu mutum ya fito gidan rediyo ko shafukan sada zumunta ya ce ‘ya kamata Shugaba Buhari ya sanya baki domin ganin an daina ficewa da abincin da aka noma zuwa kasashen ketare shi ke nan sai a ce wane ya kafirta? Ko wane dan Shi’a ne ko kuma wane munafiki ne! Ina dalilin fadin hakan?
Jama’a ya kamata mu san abin da za mu furta domin gudun aikata da na sani. Magana ta gaskiya ita ce saurin yanke hakunci ba naku ba ne domin kuwa wanda zai fito ya fadi gaskiya wallahi ya fika son Buhari domin kuwa matukar soyayyarka ga Buhari za ta sanya ka ki fadin abin da yake gaskiya to, wannan babu fa’ida ciki. Insha Allahu nan gaba kadan kowane dan kasa zai gane illar wadan nan mutanen na Abuja. Ku ne kuke tada jijiyoyin wuya kuna sai wane, sai wane, amma wallahi suna can sun gamu wuri guda suna facaka da arzikin kasa.
Adamu Aliyu Ngulde, 08032135939. <[email protected]>