Wata mai suna Pan Xiaoting, mai shekara 24 ’yar ƙasar China wacce ta yi suna wajen narkar abinci don jin burge mabiyanta ta rasu yayin da take tsaka da wurga loma ana ɗaukar bidiyonta.
Ƙasar China ta haramta nuna bidiyon nuna bajintar yawan cin abinci a shekarar 2020, a wani yunƙuri na rage yawan ci da ɓarnar abinci wanda abin kunya ne ga masu yin haka.
- Zanga-Zanga: An tsananta matakan tsaro a iyakokin Nijeriya
- Yadda Kirista ya taimaki mahaifiyar Rarara a hannun masu garkuwa
Sannan kuma duk wanda aka samu da aikata haka za a ci tararsa Dala 1,400 (kimanin Naira miliyan 2 da dubu 300 da 434.
Duk da dokar hana nuna bajintar cin abincin, hakan na ci gaba da yin tasiri da yin farin jini a ƙasashen Asiya.
Kuma yin hakan na sa dubban mutane jefa rayuwarsu a cikin haɗari ta hanyar cin abinci da yawa don burge masu kallo.
Pan Xiaoting, tsohuwar ma’aikaciyar gidan sayar da abinci ta zama ƙwararriyar wajen burge mabiyanta kan yawan cin abinci. Kuma ta rasu ne a farkon watan nan lokacin da take cin abinci ana ɗaukarta kai tsaye a bidiyo inda ta yanke jiki ta faɗi.
Binciken gawar ya nuna cewa cikinta ya cika da abinci mara narkewa kuma ya yi matuƙar cinkushewa.
Pan, bayan ta kalli masu burge jama’a lokacin da suke cin abinci da yawa da kuma suka yi nasarar rayuwa suna samun kuɗi, kuma magoya bayansu na ƙoƙarin aika musu da kyaututtuka ta hanyar ganinsu a bidiyo, sai ta yanke shawarar bin sahunsu.
Nuna bajintar cin abinci da yawa babbar gasa ce, don haka Pan ta bi sahu yayin inda take ƙoƙarin ƙara yawan mabiyanta, ta hanyar ƙara yawan abincin da take ci.
Da farko, budurwar ta dogara da shafinta na YouTube tana wallafa bidiyonta kai-tsaye idan tana cin abinci a matsayin hanyar samun kuɗi, amma da mabiyanta suka ƙaru wajen kallonta, sai ta fara kallon hakan a matsayin wata babbar sana’a.
A ƙarshe Pan ta ajiye aiki ta yi hayar wani gida da take amfani da shi a matsayin ɗakin ɗaukar bidiyonta don mabiyanta su kalla, saboda iyayenta ba su amince da sabuwar sana’arta ba domin sun damu da lafiyarta.