Wani mai bai wa jiragen sama hannun bayan sun sauka ko gabanin tashi a fili jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin kasar ya riga mu gidan gaskiya.
Aniekan Inuk Effiong, mai yi wa matuka jiragen sama jagora kan titin da ya kamata su bi gabanin tashi ko bayan sun sauka, ya yanke jiki ya fadi matacce da sanyin safiyar Litinin.
- An bukaci gwamnatin Kano ta mayar wa da Jami’ar Maitama Sule kadarorinta
- Ana fama da karancin kwaroron roba a Kenya
Aminiya ta ruwaito cewa, Aniekan Inuk Effiong ya yanke jiki ya fadi ne yana tsaka da aiki kuma tun gabanin a yi gaggawar mika shi asibiti ya ce ga garinku nan.
Kawo yanzu dai babu wata sanar da tabbatar da mutuwar ma’aikacin, sai dai bayanai sun ce marigayin daya ne daga cikin mambobin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (NAMA).
Makonni biyu da suka gabata ne wani ma’aikaci a filin jirgin saman da ke Asaba, babban birnin Jihar Delta ya riga mu gidan gaskiya.
Ma’aikacin wanda shi ma mamba ne na Hukumar NAMA, Mista Francis Anwetin, ya mutu ne a kofar shiga filin jirgin saman na Delta yayin da wata motar aiki ta buge shi.
Ya zuwa yanzu zai dai ma’aikatan NAMA biyu ke nan suka riga mu gidan gaskiya cikin tsawon lokacin da tazararsa ba ta wuce mako biyu ba.