✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahauci ya gurfana a gaban kotu kan rediyon sata

Ana zargin dan wani gungun barayin da suka addabi jama'a ne

An gurfanar da wani mahauci a gaban kotu a yankin Karu na Abuja, bisa zarginsa da mallakar rediyo da makirfon na sata.

Baya ga haka, ’yan sanda na zargin mahaucin na daga cikin gungun barayin da suka addabi mazauna yankin.

Lauya mai gabatar da kara, Edwin Ochayi, ya fada wa kotun cewa a ranar 22 ga watan Janairu aka cafke wanda ake zargi dauke da rediyo da makirfon na satar.

Laifin dai a cewarsa, ya saba wa sassa na 319 da 306 na kundin Penal Code.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Umar Mayana, ya ba da belin wanda ake zargin kan kudi N100,000 tare da shaida daya.

Bayan haka, Mayana ya dage shari’ar zuwa ranar 23 ga Fabrairu duk da dai mai kare kansa ya ki amsa tuhuma.

(NAN)