An gurfanar da wani mahauci a gaban kotu a yankin Karu na Abuja, bisa zarginsa da mallakar rediyo da makirfon na sata.
Baya ga haka, ’yan sanda na zargin mahaucin na daga cikin gungun barayin da suka addabi mazauna yankin.
- Mutum 2 sun mutu, 17 sun kamu da zazzabin Lassa a Binuwai
- Zaben 2023: Gwamnati ta ba jami’o’in Najeriya hutun mako 3
Lauya mai gabatar da kara, Edwin Ochayi, ya fada wa kotun cewa a ranar 22 ga watan Janairu aka cafke wanda ake zargi dauke da rediyo da makirfon na satar.
Laifin dai a cewarsa, ya saba wa sassa na 319 da 306 na kundin Penal Code.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Umar Mayana, ya ba da belin wanda ake zargin kan kudi N100,000 tare da shaida daya.
Bayan haka, Mayana ya dage shari’ar zuwa ranar 23 ga Fabrairu duk da dai mai kare kansa ya ki amsa tuhuma.
(NAN)