Mahara sun harbe wasu shugabannin jam’iyyar PDP biyu a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato har lahira.
An kashe shugabannin ne a lokacin da dan majalisar mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa/Bassa a Majalisar Dokokin Jihar Filato, Hon Musa Agha, ya kai ziyarar aiki a karamar hukumar.
- An sanya na’ura mai ba da fatawa da Hausa a Masallacin Harami
- HOTUNA: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad na neman takarar dan majalisa
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun lalata motar dan majalisar.
Ya ce ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka kai harin.
Kabilar Iregwe da ke Bassa ta yi Allah wadai da harin tare da yin kira ga jami’an tsaro da su gano wadanda suka kai harin.
Kazalika, jam’iyyar PDP a jihar ta yi Allah tir da harin, inda ta ce al’ummar jihar na cikin hatsari duba da yadda ake kai hari kan jama’a ba gaira ba dalili.