’Yan bindiga da suka sace tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Nasarawa, Clement Uhembe, sun nemi a ba su kudin fansa Naira miliyan 30.
Masu garkuwar sun shiga gidan Cif Uhembe wanda a yanzu malami ne a Jami’ar Gwamnatin Taraya da ke Nasarawa a daren Laraba.
“Sun zo da misalin karfe 8:30 na dare suna dukan kofa da karfi sai na je in ga ko waye sai iske mutane dauke da bindigogi.
“Da na fahimci ’yan bindiga ne, sai na yi kokarin kulle kofar da kuba ina ihu, daga nan mijina ya zo ya taya ni muka ci karfinsu muka kulle kofar”, inji matarsa, Amarya Uhembe.
Ta ce daga baya ’yan bindigar sun balle kofar suka shigo gidan sa’annan suka ce minin nata ya dauki wayarsa ya bi su.
Amarya ta ce daga baya sun kira ta suka ce ta kai musu Naira miliyan 30 kafin su sako shi.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da aukuwar lamarin.