✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun wawushe kayan abinci, sun sace mai shago a Abuja

Ana cikin Sallar Isha dandazon maharan suka shiga kwashi kayan abinci da wayoyi kimanin guda 100 da aka kawo caji a shagon

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun wawushe kayan abinci a wani shago suka kuma sace mai shagon mai suna Chinedu Arinze, a kauyen Adagba da ke yankin Abaji a Abuja.

Wani mazaunin yanin, James Gwatana, ya shaida mana cewa dandazon ’yan bindigar dauke da muggan makamai sun mamaye shagon Arinze suka kwashi kayan abinci da wayoyi kimanin guda 100, da aka kawo caji daga bisani suka yi awon gaba da shi.

Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Abaji, Abubakar Abdullahi, wanda dan yankin ne ya shaida wa wakilinmu cewa “Ina kauyen a sa’ilin da lamarin ya auku; da misalin karfe 8 na dare na soma jin harbin bindiga, daga bisani na samu labarin an sace Arinze Chinedu wanda ke da shago a yankin”.

Lamarin ya auku ne a ranar Litinin da misalin karfe 8 na dare, a daidai lokacin da ake Sallar Isha.

Duk kokarin da aka yi domin jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, DSP Adeh Josephine kan batun, abin ya ci tura.