’Yan bindiga sun kashe mutane da dama a wani hari da suka kai wa sansanin rundunar tsaron hadin gwiwa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.
Aminiya ta gano cewa kafin wayewar garin Juma’a ne ’yan bindiga suka kai hari a kan sansanin tsaron hadin gwiwa da ke kauyen Dama, inda suka kona motocin soji biyu suka kuma sace wata motar da suka yi amfani da ita wajen daukar kayan abincin sata.
- An gano maboyar gidan rediyon kungiyar IPOB
- Abin Da Shugaba Buhari Ya Fada Wa Majalisar Dinkin Duniya
Da yake tabbatar da harin, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni, Idris Muhammad Gobir, wanda aka fi sani da Danchadi, ya ce wasu daga cikin jami’an tsaron sun bace.
Ya ce sun samu tabbacin harin ne daga wani mazaunin yankin da yake amfani da layin sadarwa na Jamhuriyar Nijar.
“Amma zan tuntube shi domin samun karin bayani sannan in sanar da ku,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.
Wani basarake a yankin ya tabbatar cewa an tura motoci domin su kwashe gawarwakin jami’an tsaron da suka kwanta dama.
“Sannan motoci akalla 10 cike da sojoji suna kan hanyarsu ta shiga daji don bin sawun maharan,” inji shi.
Wani jami’in hukumar tsaro ta sibil difens, ya tabbatar wa wakilinu cewa jami’an hukumar na daga ciki wandanda suka rasa rayukansu a farmakin da ’yan bindigar suka kai wa sansanin tsaron hadin gwiwar.
A lokacin da muka tuntube shi, ya ce, “A yanzu haka mun je dakin ajiyar gawarwaki za mu kwashe su a yi musu jana’iza”.
Maharan sun kuma kai hari a kan kauyen Katsira inda suka sace mutum uku, suka harbi wasu hudu.
Biyu daga cikin wadanda aka harba sun rasu, ragowar biyun kuma ana jinyar su a asibiti.
’Yan bindiga sun yawaita kai hare-hare a yankunan Jihar Sakkwato, tun daga lokacin da aka dauki matakin toshe layin sadarwa a makwabciyarta, Jihar Zamfara, inda sojoji ke musu luugden wuta.