Kasa da awa 24 da kai harin da aka kashe mutum 16 a Karamar Hukumar Kaura ta jihar Kaduna, ‘yan bindiga sun sake kai wani hari a gundumar Gora Gan da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf.
Majiyar Aminiya ta ce maharan sun shigo ne karfe bakwai da ‘yan mintuna inda suka fara bude wuta kan mai uwa da wabi a daren Litinin.
Sai dai babu tabbacin asarar rai ya zuwa lokacin hada wannan labarin.
Gabanin nan akalla mutum 17 ne ciki har da wani sufeton ‘yan sanda aka kashe a harin da aka kai kauyen Kukum Daji da ke Karamar Hukumar Kaura a daren Lahadi.
Wata majiya kuma ta ce an kai harin ne garuruwan Kukum Daji da Manyi da ke Sabon Garin Manchok.
Maharan sun kuma jikkata wasu da dama inda aka wuce da wasu zuwa Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna, wasu 11 kuma aka kai su Asibitin Salem da ke Throneroom a garin Kafanchan.
Maharan sun isa garin Kukum Daji ne a kan babura dauke da bindigogi da misalin 10:30 na daren Lahadi inda suka bude wuta a wajen wani bikin aure da ake gudanarwa.
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Kaura, Bege Katuka Ayuba, ya ce an tafi da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke Kaduna da kuma wani a Kafanchan don ci gaba da kulawa dasu.
Bege Katuka ya ce tuni jami’an tsaro sun isa wajen inda ya yi kira ga jama’ar wurin da su kwantar da hankalinsu don ana ci gaba da bincike tare da neman maharan.
Yayin da Aminiya ta tuntuvi Kakakin Rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar harin a daya daga cikin kauyukan Kaura sai dai ya ce har zuwa lokacin hada labarin ba su tantance adadin wadanda harin ya shafa ba.
ASP Mohammed Jalige yace suna da rahoton rasa rayuka kuma tuni rundunarsu ta tura jami’anta wajen da abin ya faru kuma komai ya lafa a daidai lokacin hada wannan rahoton.