Wata rana ta fargaba ta sake kasancewa a kan al’ummar kauyen Madaka na karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja, inda wasu mahara suka yi wa awon gaba da mai garinsu, da kone gidaje gami da kashe mutane da dama.
Wannan mummunan lamari ya auku ne bayan kwana daya da wani jigo na jam’iyyar APC, Kwamared Jonathan Vatsa ya roki Shugaban Kasa Mummadu Buhari da ya kawo dauki jihar saboda gwamnan jihar ba ya da ikon magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
- Boko Haram: An kashe sojoji 5, an sace fararen hula 35 a wani sabon hari
- COVID-19: El-Rufai ya umarci ma’aikatan Kaduna yin aiki daga gida
Shugaban Ma’aikatan Ciyaman din karamar hukumar Rafi, Mohammed Mohammed ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce an kashe mutum uku – Shugaban kungiyar ’yan sa-kai a kauyen, Isiyaku Alhassan da dansa, Abdulhamid Isiyaku da kuma wani mutum guda wanda ba gano sunansa ba tukunna.
Ya kuma bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da mai garin kauyen Madaka a karo na biyu kenan bayan ya shafe sama da watanni uku a hannun masu garkuwa da mutane kafin a sake shi a kwanan nan.
A cewarsa, harin ya auku ne a tsakanin karfe 11.00 zuwa 2.00 na dare a ranar Lahadi, lamarin da ya sanya mutanen kauyen suka bazama domin tsira da lafiyarsu.
Kazalika, ya ce har yanzu ba iya kwaso gawarwakin wadanda maharani suka kashe ba.