✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kona ofishin INEC a Imo

Da talatainin dare kafin wayewar garin ranar Litinin maharan suka cinna wa ofisoshin wuta, suka kashe mutum uku a harabar ofishin.

Akalla mutum ne suka mutu yayin da wasu mahara suka kai farmaki ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), da ke kan titin Fatakwal a Jihar Imo.

Da misalin karfe 3 na talatainin dare kafin wayewar garin ranar Litinin ne maharan suka cinna wa ofisoshin wuta, suka kashe mutum uku da suka samu a harabar ofishin.

Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai yi cikakken bayani ba, amma ya ce rundunar ta ce ta cafke mutum biyu cikin maharan kuma ta baza komarta don damke ragowar da suka tsere.

Ya ce rundunar na hada bayanai, don farauto ragowar maharan da suka tsere.

Daga cikin abubuwan da maharan suka kone har da takardu, ababen hawa da sauransu, sannan suka yi wa harabar kaca-kaca, inda suka kone abubuwan amfani masu tarin yawa.

’Yan bindiga dai na ci gaba da kai hare-hare a ofisoshin INEC, musamman a yankin Kudu maso Gabas, a wani yunkuri na hana hukumar gudanar da babban zaben 2023 da ke karatowa.