Sojoji uku sun kwanta dama tare da wani dan sintiri a wani hari da ’yan bindiga suka kai garin Yakila a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.
Aminiya ta gano cewa gabanin harin ’yan bindigar sun yi garkuwa da wani mutum dan kasar China tare da Direbansa a wani wurin aikin gini a kauyen suka kuma tsere da su.
Wani shaida da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar wa da wakilanmu cewa jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a yayin da suka fito ceton dan Chinan da direbansa.
Ya ce sun rasa rayukansu yayin musayar wuta da ’yan bindigar wadanda adadinsu ya kai 30 a kan babura 15.
Kokarin tuntunbar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja domin tabbatar da lamarin bai yi nasara ba a yayin da wakilinmu bai samu jin ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ba; ASP Wasiu Abiodun.
Sai dai Hadimi na Musamman ga Gwamna Abubakar Sani Bello kan Harkokin Tsaro, Kanar MK Maikudu (mai ritaya), ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’an tsaro domin gano bakin zaren.