‘Yan bindiga ne sun kashe tsohon Shugaban Kungiyar Daliban Rigasa, Kaduna, Kwamared Auwal Rabiu Daura a tashar jirgin kasa.
‘Yan bindigar sun ji wa mutum daya rauni sannan suka yi garkuwa da wani mutum daya a lokacin harin.
- ’Yan bindiga: Gwamnatin Kaduna ta ziyarci kauyukan hanyar Abuja
- ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro uku a Kaduna
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 15 a hanyar Kaduna
- ’Yan bindiga sun kashe mai ciki sun dauke mijinta a Kaduna
Mutane ukum na cikin abin hawa yayin da ‘yan bindigar suka bude musu wuta a ranar Juma’a, daura da tashar jirgin kasa da ke Rigasa a garin Kaduna.
Yanzu haka Umar bn El-Khatab yana Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna, inda ake ci gaba da ba shi kulawa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin Abdul’Azeez Madugu (Dam Dubai), ya ce an yi jana’izar mamacin a ranar Asabar da misalin karfe 8 na safe.
Bincike ya tabbatar da cewa wanda lamarin ya ritsa da su, gaba daya mazauna yankin na Rigasa ne.
Madugu ya kara da cewa ‘yan bindiga suna yawan kai farmaki kan hanyar da ke kai mutane yankin nasu daga filin jirgin sama.
Sannan ya yi kira da Gwamnatin Jihar Kaduna da ta samo mafita dangane da ayyukan ‘yan bindiga a jihar.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin.