✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe mutum 30 a Kudancin Kaduna

Maharan sun kuma kona gidaje bayan mutanen da suka buda wa wuta.

Akalla mutum 30 ne aka tabbatar da rasuwarsu a wani hari da ’yan bindiga suka kai yanin Kudancin Jihar Kaduna.

Maharan sun kuma kona gidaje da dama a yayin farmakin da suka kai a kauyukan Madamai da Abun da ke Karamar Hukumar Kaura da Jihar a ranar Lahadi da yamma.

Tsohon Shugaban Gamayyar Matasan Yankin, Kwamred Derek Christoper, ya ce maharan sun far musu ne da misalin karfe 5 na yamma, suna harbi babu kakkuatawa a kan duk wanda suka yi gani.

“Sauran mutanen an kai su assibiti suna samun kulawar gaggawa”, inji Derek.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, amma wayarsa ba ta shiga har muka kammala hada wannan rahoton.

Harin na zuwa ne bayan wasu awanni da kai makamancinsa a wani coci a wani kauye a Karamar Hukumar Kachia.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum daya a harin da na cocin ECWA da ke kauyen Gabaciwa a Karamar Hukumar ta Kachia a ranar Lahadi da safe.