✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe mutum 5 a Kaduna

An kai harin ne dai a kan wasu manoma da yammacin Litinin a kauyen Goska dake jihar.

Wadansu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kashe mutum biyar tare da jikkata daya a wani hari da su ka kai yankin Kudancin Kaduna.

An kai harin ne dai a kan wasu manoma da yammacin Litinin a kauyen Goska da ke Karamar Hukumar Jama’a ta jihar Kaduna.

Wata mata da ta bukaci a sakaya sunanta daga kauyen ta shaidawa Aminiya cewa maharan sun afko musu ne da adduna da wukake da bindigogi inda suka far musu a gona.

Hakan, a cewarta ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu a nan take,  yayin da na biyar din kuma ya cika a gadon asibiti daga bisani.

“A yanzu haka an kwashe gawar mutane hudun da aka kashe tare da na mutane biyun da aka jikkata zuwa Babban Asibitin garin Kafanchan inda daya daga cikin wadanda aka jikkata ya cika a can” inji ta

Sai dai duk kokarin Aminiya na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sanda ta jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya ci tura har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.