✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 46 a Binuwai

’Yan bindiga sun kashe akalla mutum 46, ciki har iyalan Shugaban Karamar Hukumar Otukpo na Jihar Binuwai

’Yan bindiga sun kashe mutum 46 a yayin da ake tsaka da zaman makokin wasu da ’yan bindiga suka kashe a Karamar Hukumar Otukpo na Jihar Binuwai.

Shugaban Karamar Hukumar Otukpo na Jihar Binuwai, Bako Eje, ya shaida wa wakiliyarmu ta waya cewa dansa da wasu danginsa na daga cikin mutanen da aka kashe a harin.

Ya ce ana tsaka da zaman makokin mutanen da aka kashe ne a yammacin ranar Laraba maharan suka yi wa kauyen kawanya, suka bude wa jama’a wuta.

Bako Eje ya ce maharan sun kai farmakin ne a kauyen Entekpa-Adoka da ke karamar hukumar a ranar Laraba, washegarin da aka kai wani hari, aka kashe mutum uku.

Ya bayyana cewa kawo yanzu an gano gawarwakin mutum 46, amma akwai wasu mutane da dama da suka bace.

Shi ma da yake bayani, mai ba wa gwamnan jihar shawara kan tsaro, Laftanar Kanar Paul Hemba, ya ce akwai yiwuwar adadin wadana aka kashe a harin ya karu.