✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Mahara sun kashe mutum 37 a Nijar

Maharan sun hallaka mata da kananan yara a gonakinsu.

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa wasu mahara sun kashe mutum 37 a kauyen Darey Dey da ke yankin Banibangou a Jihar Tilaberri, wanda ke da iyaka kasar da Mali.

Bayanai sun ce daga cikin mutanen da maharan, wadanda ke yawo a kan babura, suka ka kashe har da kananan yara 14 da kuma mata hudu a gonakinsu.

– Tankar mai ta kashe mutum 2 ta kona motoci 14
Na so a ce ’yata ta kammala karatu kafin ta auri dan Buhari – Sarkin Bichi

Wasu ganau sun ce maharan sun bude wuta a kan jama’ar ne a yammacin ranar Litinin.

Harin na ranar Litinin shi ne irinsa na biyar a baya-bayan nan wanda aka mutane da dama a yankin na Tillaberi da yawansu ya kai 151 zuwa yanzu.

Alkaluma sun nuna adadin mutanen da mahara suka kashe a yankin ya kai 450, tun daga farkon shekarar nan zuwa yanzu.