✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mutum 28 a Kudancin Kaduna

Mutum 28 sun mutu, an jikkata  wasu da dama a wani harin ’yan bindiga a kauyukan Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Mutum 28 sun mutu, an jikkata wasu da dama a harin ’yan bindiga a kauyukan Malagum 1 da Sokwong na Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Sakataren Karamar Hukumar, Raymond Ibrahim, ya ce ’yan bindiga sun far wa kauyen Sakwong ne da misalin karfe 12 na dare kafin wayewar garin Lahadi, suna harbi kan mai uwa da wabi tare ne cinna wa gidade da dukiyoyi wuta.

Ya ce, “Da safen yau muka dawo daga wurin muka ga gawarwaki tara, daga nan muka karasa zuwa kauyen Malagum 1 inda ganau suka tabbatar mana cewa an kashe mutum 19.”

Raymond Ibrahim ya ce an kai harin ne kwana biyar bayan wani da aka kai a Malagum 1 aka kashe mutum hudu.

Jami’in ya bukaci mutanen su kwantar da hankalinsu, sannan ya roki gwamnati ta kawo dauki ga mutanen yankin da suka rasa muhallansu.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige, domin karin bayani, amma bai amsa waya ba.