Mutum 28 sun mutu, an jikkata wasu da dama a harin ’yan bindiga a kauyukan Malagum 1 da Sokwong na Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.
Sakataren Karamar Hukumar, Raymond Ibrahim, ya ce ’yan bindiga sun far wa kauyen Sakwong ne da misalin karfe 12 na dare kafin wayewar garin Lahadi, suna harbi kan mai uwa da wabi tare ne cinna wa gidade da dukiyoyi wuta.
- Sabon rikici ya kunno kai a PDP ta Kano kan ba ’yan takara tuta
- Hatsarin mota: Mata 11 sun kone kurmus a hanyar Zariya zuwa Kano
Raymond Ibrahim ya ce an kai harin ne kwana biyar bayan wani da aka kai a Malagum 1 aka kashe mutum hudu.
Jami’in ya bukaci mutanen su kwantar da hankalinsu, sannan ya roki gwamnati ta kawo dauki ga mutanen yankin da suka rasa muhallansu.
Wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige, domin karin bayani, amma bai amsa waya ba.