✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe mutum 20 a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe mutum 20 a Karamar Hukumar Talata Mafara ta Jihar Zamfara

’Yan bindiga sun hallaka mutum 20 a harin da suka kai kauyen Tungar Kwana a Karamar Hukumar Talata Mafara ta Jihar Zamfara.

Mahara dauke da makamai sun shiga garin a kan babura suna ta harbi kan mai uwa da wabi.

“An riga an binne wadanda suka mutu kuma yawancin mazauna sun yi kaura.

“Muna roko a turo mana karin jami’an tsaro a yankin”, inji wani daga cikin mazauna garin, Halilu Adamu.

Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun tare hanyoyin ficewa daga garin sannan suka yi awon gaba da dabbobi da yawa.

Ana ganin an kai musu harin ne saboda mazauna sanar da jami’an tsaro maboyar ’yan bindigar da suka kai wa farmaki a makon jiya.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara, Muhammad Shehu, ya ce tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce al’amura sun fara daidaita.