✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe mutum 2 sun sace 13 a Sakkwato

Maharan sun yi awon gaba da dabbobi da wayoyin hannu da dukiyoyin mutanen yankin Gwadabawa

’Yan bindiga dauke da manyan makamai sun kashe mutum biyu sun yi garkuwa da 13 a yankin Mammansuka a Karamar Hukumar Gwadabawa ta Jihar Sakkwato.

Maharan sun zo da yawan gaske, suka ci karensu babu babbaka, inda suka tafi mata 11 da namiji biyu a satin da ya gabata.

Shugaban Karamar Hukumar Gwadabawa, Aminu Aya, ya ce bayan mutanen da suka kashe suka yi garkuwa da 13 sun tafi da dabbobi da wayoyin hannu da dukiyoyin mutanen yanki.

Shugaban ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa su kawo dauki ga mutanen karamar hukumarsa ganin aikin ta’addanci ya zama abin da ake yi kullum.

Ya ce akwai bukatar a yi kokari a kwato mutanen da aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya su dawo cikin iyalansu.