Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wajen wani taron shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar a Karamar Hukumar Enugu ta Kudu, inda suka bude musu wuta wanda a dalilin haka mutum biyu suka riga mu gidan gaskiya.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba a ofishin jam’iyyar APC da ke mazabar Obeagu Awkunanaw a jihar, inda kuma ‘yan bindigar suka yi awon gaba da wani mutum daya.
- An shawarci Buhari ya mayar da farashin man fetur zuwa N302 duk lita
- Yadda Abacha ya yaudari ’yan Najeriya ya hau mulki —IBB
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar kusan mutum bakwai sun kashe mutum biyu sannan sun raunata wasu da dama yayin da suka yi awon gaba da mutum daya daga cikin shugabannin na APC na mazabar.
Wata majiya ta bayyana cewar an shirya taron ne don yin sulhu tsakanin mambobin jam’iyyar da ke samun sabani a tsakaninsu.
Daya daga cikin wadanda ‘yan bindigar suka kashe shi, tsohon shugaban jam’iyyar ne na karamar hukumar, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban matasa na jam’iyyar na jihar a yanzu, Mista Kelvin Ezeoha.
Sai dai ana zargin ‘yan kungiyar awaren Biyafara da hannu wajen kai harin, wanda ake zargin na da alaka da siyasar jihar, bayan sake sanya dokar zaman gida da IPOB din ta yi a ranar Litinin.
Kawo wannan lokaci na hada wannan rahoto mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.