✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe mutum 1 sun sace wasu 6 a Neja

Maharan sun far wa garin da tsakar dare suna harbi kan mai uwa da wabi.

Mahara bindige mutum daya suka kuma yi garkuwa da wasu mutum shida a kauyen Guba-Abugi na Karamar Hukumar Lapai a Jihar Neja.

Gungun yan bindigar, dauke da muggan makamai sun kai harin ne bayan kwana daya da nada sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro.

“Dandazon maharan sun shigo ne da misalin karfe 1:00 na dare, suna harbi ta ko’ina, wanda hakan ya sa mutane suka yi ta guje-gujen tsira da rayukansu; amma an kashe mutum daya an kuma yi garkuwa da wasu shida,” inji wani mazaunin garin mai suna, Idris Musa Avu.

Ya ce ’yan banga sun yi iya kokarinsu a lokacin da aka kai harin, sai dai ba sa samu gudunmuwa daga ’yan sanda ba.

Aminiya ta yi ta kokarin samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan a Jihar Neja, ASP Wasiu Abiodun amma ba ta same shi ba.

Wayarsa ta kasance a kashe har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoton.