’Yan bindiga sun aika mutane biyu lahira a kauyen Dagwarga, tare da yin garkuwa da wasu 19 a Maraban Walijo a Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.
Da yake zantawa da wakilinmu a ranar Talata, wani mazaunin garin Dagwarga, Alhaji Abdullahi Abubakar, ya ce da alamar harin da ’yan bindiga suka kai Dagwarga ramuwar gayya ce.
“’Yan bindigar sun kai hari a Maraban Walijo ranar Lahadi inda suka yi awon gaba da mutane 19.
“Amma a yayin harin, al’ummar garin sun yi nasarar kashe daya daga cikin ’yan bindigar.
- An kama ’yan talla da ke kai wa ’yan bindiga bayanai
- An ceto ’yar shekara 2 da maƙwabcinsu ya sace ta a Kano
“Sun dawo ne ranar Litinin domin daukar fansa, amma saboda tsananin matakan tsaro a Maraban Walijo, suka kawo mana hari a Dagwarga, saboda ba mu da nisa daga Maraban Walijo,” in ji shi.
Maharan, a cewar Abubakar, sun mamaye kauyen Dagwarga da misalin karfe 2:00 na dare kafin wayewar garin Litinin inda suka fara harbe-harbe, nan take suka kashe mutum biyu.
“Dazun nan muka binne su a makabartar Dagwarga bisa tsarin addinin Musulunci,” in ji Abubakar.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, Mansir Hassan, bai amsa kiran da aka yi masa kan wannan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.