✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe manoma uku a gonakinsu a Birnin Gwari

An kashe su ne lokacin da suke aiki a gonakin nasu

’Yan bindiga sun kai wani sabon farmaki inda suka kashe manoma uku a gundumar Sabon Layi da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da tsakar ranar Alhamis, kamar yadda wasu majiyoyi a yankin suka tabbatar.

Shugaban Kungiyar Bunkasa Masarautar Birnin Gwari (BEPU), Usman Kasai, ya tabbatar da kai harin, inda ya ce an kashe manoman ne lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu.

Ya ce mutanen da aka kashe sun hada da Anas Sabon Layi da Abubakar Dankibiya da kuma Harisu Unguwar Lemu.

Dukansu mazauna gundumar Sabon Layi ne da ke karkashin mazabar Kakangi.

Yanzu haka dai ana ci gaba da fargabar yiwuwar kai karin harin a yankin cikin’yan kwanaki masu zuwa.

Ko a makonnin da suka gabata, sai da aka kai makamancin wannan harin inda aka kashe mutum tara, lamarin da ya tilasta da yawa daga cikin manoman barin gonakinsu.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu wanda ya magantu tsakanin Gwamnatin Jihar da kuma Rundunar ’Yan Sandan Jihar a kan harin.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar, Mohammed Jalige, ya ce yanzu haka yana masallaci.