✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Gombe Za Ta Kafa Hukumar Safarar Magunguna Da Kayayyakin Jinya

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya sa hannu kan dokar kafa hukumar kula da safarar magunguna da kayayyakin jinya a jihar. Kakakin gwamnan, Isma’ila…

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya sa hannu kan dokar kafa hukumar kula da safarar magunguna da kayayyakin jinya a jihar.

Kakakin gwamnan, Isma’ila Uba Misilli ne ya bayyana haka a sanarwar da ya rabawa ƴan jaridu.

Sanarwar ta ce tun ranar 18 ga Mayu Majalisar Dokokin jihar Gombe ta amince da ƙudirin dokar.

Matashiya mai yi wa kasa hidima ta mutu a Gombe

Majalisar Gombe ta amince Gwamna ya nada mashawarta 30, ya kara wa Ciyamomi wa’adi

Haka kuma  ta ce hukumar za ta kasance sahihiyar hanya ta samar da magunguna da kayayyakin jinya masu inganci da rahusa ga al’ummar jihar.

Bayan haka, sanarwar ta buƙaci haɗin kan al’amu domin samun nasarar hukumar.