Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kama wani matashi da ke yi wa jami’an tsaro sojan gona a unguwar Madaki da ke jihar.
An cafke matashin mai shekaru 32 dan asalin Jihar Benuwe da ke sojan gona a matsayin jami’in tsaro yana safarar tabar wiwi.
- An kama matasa 3 kan zargin kashe dilan tabar wiwi a Gombe
- Jerin Kasashen Da Aka Haramta Bikin Ranar Masoya
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya tabbatar da hakan yayin da yake yi wa manema labarai holen matashin da sauran ababen zargin da suka shiga hannu.
ASP Mahid ya ce ’yan sanda sun kama matashin ne zai tafi garin Guyuk da ke Jihar Adamawa da ƙunshin tabar wiwi guda shida da kuma hular sojoji.
A zantawarsa da Aminiya, matashin ya ce lallai ya san ya yi laifi na yin sojan gona a matsayin dan sanda mai mukamin ASP 1.
Matashi ya ce ya yi hakan ne saboda kaucewa dogon binciken da jami’an tsaro ke yi a kan hanya “domin idan kai ba wani ba ne a lokacin da kake tafiya a hanya jami’an tsaro suna yawan binciken mutum a abun hawansa.”
Ya ce hular sojan da aka kama shi da ita sa wa kawai ya yi a motarsa amma ba tasa ba ce.
Sai dai ya ce katin shaidar dan sandan nasa ne domin hotonsa ne a jiki, don haka yake neman afuwar ’yan sanda kan wannan kasassaba da ya yi.
Ya ce tsautsayi ne ya haushi domin shi ba halinsa ba ne kuma a cewarsa ko lokacin da aka kama shi aka kai shi gidansu kowa ya yi mamaki saboda ba a san shi da shiga irin wannan harkar ba.
Da yake bayyana nadamar laifin da ya aikata, matashin ya ce ya yi sojan gonar ne domin ya riƙa wucewa da tabar wiwi salin-alin ba tare da jami’an tsaro sun riƙa tare shi suna bincikarsa ba kamar yadda ake yi wa fararen hula.
Ya kara da cewa, yana roƙon ’yan sanda da su yi masa afuwa domin wannan shi ne karo na farko da ya taba aikata irin wannan laifi.
Daga bisani kakakin rundunar ’yan sandan ya ce idan suka gama binciken za su tura shi kotu domin ya girbi abin da ya shuka.