✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe Fulani makiyaya biyar tare da sace shanu 278 a Filato

Wasu mahara da ake zaton ’yan kabilar Tarok ne sun kai wa wasu Fulani makiyaya hari a yankin Yelwan Shendam da ke karamar Hukumar Shendam…

Wasu mahara da ake zaton ’yan kabilar Tarok ne sun kai wa wasu Fulani makiyaya hari a yankin Yelwan Shendam da ke karamar Hukumar Shendam a Jihar Filato a yammacin Asabar da ta gabata, inda suka kashe mutum biyar tare da sace shanu 278.
Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah reshen Jihar Filato Alhaji Haruna Boro Hussaini ya bayyana wa Aminiya cewa a yammacin ranar Asabar kusan karfe 4:00, wasu mutane dauke da bindigogi sun auka wa Fulaninmu a Yelwan Shendam suka kashe mutum biyar suka sace shanu 278 suka gudu zuwa karamar Hukumar Langtang ta Kudu.
Ya ce babu wani kokwanto maharan ’yan kabilar Tarok ne daga Langtang ta Kudu.
Alhaji Hussaini Boro ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin dakatar da kashe- kashen da ake yi wa al’ummar Fulani da suka ki ci suka ki cinyewa a Jihar Filato.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Filato DSP Abu Emmanuel ya tabbatar da kai harin, amma bai yi karin bayani kan wadanda aka kashe ko shanun da aka sace ba.