✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe fasinja 2, sun sace 40 a Taraba

Maharan sun bude wa motar hayar wuta, nan take mutum biyu suka sheka lahira, suka kuma yi awon gaba da mutum 40.

Wasu mahara sun kashe fasinja biyu tare yin garkuwa da mutum 40 a kan titin Gembu zuwa Bali a Jihar Taraba.

A yammacin ranar Laraba ne ’yan bindigar suka tare hanyar Jamtari/Gayam da ke kan titin Gembu zuwa Bali, inda suka sace fasinjoji sannan suka yi daji da su.

Aminiya ta gano cewa maharan sun bude wa motar wuta ne, wanda hakan ya tilasta wa direban tsayawa, a sakamakon hakan kuma fasinja biyu suka ce ga garinku nan.

Wadanda aka yi garkuwa da su din sun hada da mata da kananan yara, kuma tuni maharan suka shiga da su zuwa cikin dajin mai da tsaunuka da duwatsu.

Ana zargin maharan na daga cikin ’yan bindigar da suka yi kaura daga jihohin Zamfara da Katsina zuwa Jihar Taraba a baya-bayan nan.

Masu ababen hawa sun kaurace wa hanyar a yammacin na ranar Laraba, bayan samun labarin harin.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ce ba shi da tabbacin adadin fasinjojin da aka sace.

“An tabbatar da samun labarin hari da aka kai Jamtari/Gayam da ke kan titin Bali zuwa Baruwa, amma ba mu san mutum nawa aka yi garkuwa da su ba,” cewarsa.