✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun harbe soja har lahira a Filato

Maharan sun yi awon gaba da bindigar sojan da suka bindige a lokacin da ya je aiki a gonarsa.

Wani soja mai mukamin Kofur ya gamu da ajalinsa bayan yan bindiga sun bude masa wuta har lahira a gonarsa a Jihar Filato.

Maharan sun kuma sace bindigar Kofur Folorunsho Lukman bayan sun bindige shi a lokacin da ya je aiki a gonarsa.

Lamarin ya faru ne a kauyen Kampani Zurak da ke Masarautar Bashar, a cewar majiyarmu.

Wakilinmu ya gano cewa Kofur Folorunsho Lukman ya samu izinin daga kwamandansa domin fita daga sansanin sojoji zuwa harkokinsa  na kashin kansa.

Sakamakon haka ya je dauki wasu fararen hula biyu domin yi masa kwadago a gonarsa.

A gonar ce maharan suka bullo daga cikin daji suka harbe shi har lahira sannan suka yi awon gaba da bindigarsa.

Majiyarmu ta ce Kofur Lukman Folorunsho wanda ke aiki a sansanin sojojoji na Kampany Zurak shi ne kadai ya rasu a harin, amma ’yan kwadagon sun tsira da ransu.

“Da samun labarin runduna ta biyu ta tura sojoji zuwa wurin aka dauko gawarsa,” gami da kokarin kwato bindigarsa da aka dauke, in ji majiyar sojin.

Kakakin Rundunar Operation Safe Haven, Manjo Samson Zakhom, bai fitar da sanarwa game da lamarin ba, har zuwa lokacin da muka kammala wannan labarin.

Amma ya ba da tabbacin yin karin haske da zarar ya samu bayanan da yake bukata game da harin.