✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun daba wa malamin Jami’ar Bayero wuka, sun raunata matarsa

Wasu gungun ’yan ta’adda dauke da makamai sun afka gidan wani lakcara na Sashen Nazarin Aikin Jinya a Jami’ar Bayero da ke Kano suka daba…

Wasu gungun ’yan ta’adda dauke da makamai sun afka gidan wani lakcara na Sashen Nazarin Aikin Jinya a Jami’ar Bayero da ke Kano suka daba masa wuka.

Wata majiya mai kusanci da wanda abun ya shafa ta shaida wa jaridar Sahelian Times cewa, ’yan ta’addan sun kutsa kai ne gidan malamin da ke Unguwar Shagari Quarters a Karamar Hukumar Tarauni da misalin karfe 3.00 na dare, suka rika daba masa wuka a kirji da wuya.

Wannan aika-aikan ya gadar wa da malamin mai suna Hussaini raunuka caba-caba a fuskarsa da kuma kansa.

’Yan ta’addan su shida sun kuma lakada wa matar malamin dukan tsiya, lamarin da ya kai ta samu raunuka a fuskarta.

Rahotanni sun bayyana cewa gungun ’yan ta’addan sun nemi Malam Hussaini da ya tsakuro musu wani abu daga cikin kasonsa na basussukan albashi da Gwamnatin Tarayya ta Malaman Jami’o’i a ’yan kwanakin nan.

Sai dai ya mayar musu da martanin cewa ba shi da wasu kudi masu yawa da har zai iya tsakuran musu wani abu a ciki, lamarin da fusata  su, suka tara masa gajiya shi da matarsa.

Daga bisani kuma suka arce da wayarsa ta salula, mukullin mota da wasu ’yan kudade.

Majiyar ta kara da cewa, sun yi niyyar ganin bayansa amma ya yi sa’a yana da ragowar kwanaki.