’Yan banga biyu sun kwanta dama a yayin wani artabu da suka yi da ’yan bindiga a yankin Mayaki da ke Karamar Hukumar Lapai ta Jihar Neja.
Wasu mazauna yankin da aka zanta da su, sun ce lamarin ya faru ne da safe lokacin da wasu ’yan bindiga suka yi wa wasu ’yan banga da ke sintiri kwanton bauna a ranar Lahadi.
- An yi garkuwa da tsohon Manajan gidan Talabijin na Katsina
- Dan kwallon Faransa ya rasu bayan shekara 39 a sume
Wani mazaunin yankin mai suna Ahmadu ya ce, “Al’umma gaba daya sun shiga firgici saboda harbe-harben bindiga da aka yi tsakanin ’yan banga da ’yan bindigar. Abin takaici kuma shi ne biyu daga cikin ’yan banga sun kwanta dama.”
Ya ce daga baya ’yan bindigar sun tsere daga yankin na Mayaki, da suka fahimci cewa ’yan bangar za su samu dauki daga abokan aikinsu da ke kauyen Kapako.
Yankin Mayaki na da iyaka da Jama’ar Gwaje, karkashin gundumar Gurdi a Karamar Hukumar Abaji da ke Birnin Tarayya.
Kwamandan ’yan sintiri na Jihar Neja, reshen Lapai, Muhammadu Ibrahim, ya ce, “Gaskiya ne biyu daga cikin mutanenmu sun kwanta dama a yayin sintiri, bayan wani kwanton bauna da ’yan bindiga suka yi musu a dajin Mayaki.
“Yanzu haka da nake magana da ku, mun riga tattaro mambobinmu kuma mun fara farautar wadannan miyagun domin ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai mun kamo su,” .
Mun neni kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja, ASP Wasiu Abiodun, amma bai dauki waya ko amsa rubutaccen sakon da muka aika masa ba don yi mana karin bayani game da faruwar lamarin.