Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum tara a wasu hare-haren da suka kai a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a Jihar Kaduna.
Jami’an tsaro sun cewa ’yan bindigar sun shiga yankin Dogon Dawa zuwa Kuyello da ke kauyen a Birnin Gwari, inda suka harbe mutane shida.
- Za a gwangwaje malamai da kyautar motoci
- Tallafin man fetur na lakume N120bn a duk wata
- Sojoji sun hallaka ‘yan biniga a Binuwai
- Faransa za ta taimaka wa Najeriya yaki da fashin teku
Aminiya ta gano wadanda suka rasa rayukansu sun hada da; Nura Rufai, Sanusi Gajere, Yakubu Labbo, Usman Dangiwa, Alhaji Abdulhamid da Janaidu Tsalhatu.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, inda ya ce an kuma kashe mutum biyu a Ungwan Maje.
Ya kara da cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya karbi rahoton faruwar lamarin cikin fushi da bacin rai, tare da addu’a ga wanda suka rasu da iyayensu.
Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun da Kajuru, na daga cikin kananan hukumomin da ’yan bindiga suka addaba a jihar.