✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun bindige mutum 65 a asibiti da kasuwar Sakkwato

Sun kashe mutane a cikin asibiti bayan awa biyu suna barna a Kasuwar Goronyo.

Mahara sun kashe sama da mutum 65 a Babbar Kasuwar Goronyo da ke Karamar Hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato.

Maharan sun kuma yi wa wani asibiti dirar mikiya, inda suka bude wa mutane wuta, jim kadan bayan farmakin da suka shafe kusan awa biyu suna cin karensu babu babbaka a kasuwar a lokacin da mutane ke tsaka da cinikayya.

Majiyarmu ta ce, “A lissafin da muke da shi mutanen da aka kashe sun fi 65; A gabana mun lissafa gawa ta kai 65, ba mu sanya mutanen Bodinga da Shinaka da wasu da ke cikin garin goronyo da sauran wasu da ke zuwa cin kasuwar garin.

“A jiya (Lahadi) da lamarin ya faru kasuwar ta cika sosai ganin wasu kananan kasuwanni sun daina ci kan matsalar tsaro sai ga wadannan bata-garin sun zo.”

Majiyar ta ce maharan sun tare daukacin kofifin kasuwar guda bakwai, suna harbin duk mutumin da ya yi yunkurin tserewa.

Embed code:

“Maharan sun shigo a kasuwar ne a jiya Lahadi ana kusa da tashi a kasuwa Magrib ta matsa kusa; An rika ganin wasu da kayan mata suna zagaya kasuwar a lokacin da suka isa wurin masu sayar da dusa, suka fara harbi ta ko’ina.

“Nan take ’yan uwansu suka shigo kasuwar ta kowace kofa a kasuwar suka rika harbi kan mai uwa da wabi a jiyan da dare, kai tsaye an dauki gawa ta fi 40”, a cewar ganau.

Sun ce maharan sun shafe sama da awa biyu suna cin karensu babu babbaka a kasuwar, kafin su kutsa wani asibiti su bude wa mutane wuta, sannan suka keta ta garin Kumaji suka wuce.

Wani ganau da mukan zanta da shi ya ce shi kansa ya rika kallon su ne daga wurin da ya labe.

Gwamnan Jihar Sakkwari, Aminu Waziri Tambuwal, ya tabbatar da aukuwar harin, amma tare da bayyana cewa mutum 30 ne suka rasa rayuwarsu.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a lokacin da Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Janar Faruk Yahaya ya kai masa ziyara a ranar Litinin.