Wasu gungun mayaka sun bindige akalla mutum 40 a kauyukan da ke yankin Tahoua da ke Jamhuriyar Nijar.
An gwabza kazamin fada tsakanin sojojinta da maharan a safiyar Litinin a yankin na Tahoua mai makwabtaka da iyakan kasar da Mali, a cewar kakakin Gwamnatin Jamhuriyar Abdoulraman Zakaria.
Yadda mutanen Jingir suka yi wa ’yan bindiga kofar rago
Gobara ta tashi a Babbar Kasuwar Katsina
Muna jiran hujjar Ortom cewa Fulani sun kai mishi hari —Matasan Arewa
A baya-bayan nan, ana yawan kai hare-hare a yankunan Jamhuriyar Nijar masu makwabtaka da iyakarta da kasa Mali.
Ko a ranar 16 ga Maris, 2021, wasu mayaka sun bindige ’yan kasuwa 58 a yankin Tillaberi, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar.
Kungiyoyi masu dauke da makamai sun addabi kasar da makwabtanta da ke yankin Sahel, inda wasu daga cikin kungiyoyin suka yi mubaya’a ga kungiyar IS, wasunsu kuma ga kungiyar al-Qaeda.
Gwamnati ba ta fiye nuna karfin ikonta a yankunan da ke cikin dazuka a sahara ba, kamar yadda take yi a birane.
Ana ganin hakan ce ta sa mayaka masu ikirarin jihadi saura masu aikata miyagun laifuka, ciki har da masu fasakwauri, suke amfani da damar wurin sheke ayarsu.