✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun babbake Babbar Kotun jihar Imo

Maharan sun kone ilahirin wajen adana muhimman takardu na kotun

Mahara a ranar Asabar sun kai farmaki ginin Babbar Kotun Jihar Imo da ke Orlu, inda suka kone wani sashe nata.

Wakilinmu ya cewa maharan sun kone wani sashen ginin kotun ne wanda ke dauke da wasu muhimman bayanai.

Hakan na zuwa ne ’yan kwanakin bayan wasu maharan sun kai hari tare da kone hedikwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Owerri, babban birnin jihar.

Sashen kotun da suka kona dai nan ne yake dauke da Kotun Majistare da Babbar Kotun jihar da kuma inda ake adana muhimman takardu.

Wani ma’aikacin bangaren shari’a a jihar wanda ya zanta da wakilinmu bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba ya ce ilahirin wajen da ake ajiye takardun ya kone kurmus.

Babbar Kotun da ke Orlu dai na kusa da wani shingen jami’an tsaro da kuma wani babba ofishin ’yan sanda.

Ko a ranar 1 ga watan Disamban 2018, sai da aka kone ofishin INEC da ke yankin na Orlu ta irin wannan hanyar.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, CSP, Mike Abattam, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar harin, ya ce tuni jami’ansu suka kaddamar da bincike a kai.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga gano wanda da cinna wutar ba, kuma babu wanda ya dauki alhakin kunna ta, kodayake an sha zargin mambobin haramtacciyar kungiyar nan ta ’yan awaren Biyafara ta IPOB, da irin wannan ta’asar.